Maganin Dexamethasone zai taimaka wajen ceto ran masu cutar Covid19

An gano wani magani mai suna Dexamethasone zai taimaka sosai wajen ceto ran masu tsananin fama da kwayar cutar coronavirus, kamar yadda masana kimiyya a Burtaniya suka bayyana.

BBC ta rawaito cewa, daya daga cikin masu binciken, Professor Martin Landray na Sashen Ilimin Kiwon Lafiyar Al’umma a Jami’ar ta Oxford ya ce sakamakon da suka samu daga gwajin maganin ya ba su mamaki.

Ya kuma ce Dexamethasone magani ne mai saukin samu, wanda kuma ba shi da tsada, saboda haka sakamako ne mai dadin ji.

Sai dai tilas ne a ci gaba da neman wani maganin domin Dexamethasone ba zai warkar da dukkan masu fama da cutar ba.

Na farko ba zai dace da kowane irin nau’i na wadanda ke dauke da cutar ba.

Amma abu ne mai karfafa gwuiwa idan aka tuna cewa a makon jiya-jiyan nan bamu da magani ko daya da za mu iya dogara da shi wajen yaki da annoba ta Covid19.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More