Magoya bayan PDP 300 aka kama a Bauchi

Dan takarar jam’iyyar  ta PDP a jahar Bauchi Sanata Bala Muhammad Kaura, ya yi zargin cewa ‘yan sanda sun kama magoya bayansa fiye da 300 a cikin jahar.

Jam’iyyar ta PDP ta yi wannan zargi ne a wani taron manema labarai da ta gudanar a birnin Bauchi a ranar Alhamis.

Ya yi zargin cewa ana tsare da magoya bayan jam’iyyarsu ta PDP, yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jaha.

Muhammad Abdullahi Abubakar, na jam’iyyar APC wanda ke neman wa’adi na biyu ya shaida wa Is’haq Khalid cewa an fara kama magoya bayan nasu ne tun kimanin makwanni biyu da suka gabata kuma ana ci gaba da kamen.

Zuwa yanzu rundunar ‘yan sandan jahar ba ta ce komai ba game da zargin, amma kwamishinan watsa labarai na jahar Bauchi, Umar Muhammad Sade, ya musanta zargin, yana mai cewa duk wanda jami’an tsaro suka kama, mutum ne da ake zargi da aikata laifi.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More