Majalisa ta amicewa shugaba Buhari ciyo bashin naira biliyan 850

Majalisar dattawan Najeriya ta amince wa shugaban kasar Najeriya  Muhammadu Buhari ya karbo rancen kudi naira biliyan 850.

Majalisar ta amince da bukatar ne a zaman da ta yi ranar na  Talata 28 ga watan Aprilu 2020, bayan ta dawo daga hutun Coronavirus.

Shugaba Buhari ya bukaci majalisar ta amince da bukatarsa ta samun rancen daga kasuwar kudi ta cikin gida domin bai wa gwamnatinsa damar aiwatar da kasafin kudin 2020.

Faduwar farashin danyen mai ya sa gwamnatin Najeriya ba za ta iya aiwatar da kasafin kudinta ba na shekarar 2020 ba tare da ta nemi taimako ba.

Gwamnatin ta tsara kasafin ne kan dala 57 duk ganga kafin sake sauya hasashen zuwa dala 30 duk ganga.

Yanzu kuma farashin danyen danyen mai ya fadi zuwa dala 20 duk ganga a ranar Talata.

Farashin man na ta faduwa ne sakamakon annobar Coronavirus  da take yi wa fannonin rayuwa daban-daban da suka hada da na tattalin arzikin rugu-rugu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More