Majalisa ta gabatar da kudurin  da zai  hana amfani da jannareto

Menene ra’ayinku game da hakkan?

Majalisar dattawa ta gabatar da kudurin da zai hana amfani da injin wuta na jannareto a Najeriya a ranar Laraba 11 ga watan Maris 2020.

Dan majalisa mai wakiltar Neja ta Kudu, Sanata Bima Muhammadu Emagi na jam’iyyar APC ne ya gabatar da kudurin, kuma shine karo na farko a zauren majalisar ta dattijai.

Rashin wutar lantarki yana daya daga cikin babban kalubalen da ‘yan Najeriya ke fuskanta shekaru masu yawan da suka shude.

Wannan dai na zuwa ne yayin da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta nuna cewa tana yin iya bakin kokarinta wajen ganin ta dai-daita lamarin na wutar lantarki a fadin kasar ta Najeriya.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More