Majalisa ta nemi a daina kayyade shekarun neman aikin  a Najeriya

Menene ra’ayinku game da hakkan?

 Majalisar Dattawa ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari da ya umarci Ma’aikatar kwadago da ta kafa wani kwamiti da zai duba daina amfani da kayyade shekarun neman aiki a kasar.

Majalisar ta cimma wannan matsaya ne biyo bayan kudirin da Sanata Ibrahim Gobir ya gabatar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Sanatan ya ce “‘yan Najeriya da dama na rage shekarunsu na haihuwa a kokarinsu na shiga cikin rukunin wadanda za a dauka aikin”.

Ya jara da cewa: “Duk sanda mutum ya san cewa ba za a ɗauke shi aiki ba to zai bi wasu hanyoyi da ba su dace ba, abin da ke jawo karuwar aikata laifuka da kuma rashin tsaro a kasar.”

Da yake magana yayin yin kiran, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya yi Allah-wadai kan yadda ake nuna wa wasu masu neman aiki wariya saboda shekarunsu.

“Babu laifin da suka aikata da zai sa a nuna musu wariya. Sai ka ji an ce ‘yan shekara 30 kawai ake neman; sai ka tarar wani shi kuma ya gama jami’a shekara 10 da suka wuce,” in ji shi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More