
Majalisar dattawa na shirin ware wa yan’sanda kudi na musamman
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Ibrahim Lawan ya bayyana cewa za su ware wa ‘yan sanda kasafin kudi na musamman don ganin sun aiwatar da ayyukan bisa yadda doka ta tanadar,ya bayyana haka ne a lokacin da babban Sufetan ‘yan sandan Najeriya Muhammad Adamu da tawagarsa suka kai suka ziyarci offishin sa dake babban birnin tarayyar Abuja.
Hakan yasa suka tattauna batun wata doka da ta shafi makarantar horar da ‘yan sanda da kuma asusu na musamman ga ‘yan sandan kasar ta Najeriya.
Sanata Ahmed Lawal yace, akwai bukatar sake tsarin tafiyar da ayyukan ‘yan sanda a kasar don ganin sun sami horon da ya kamata, tare da kulawa.