
Majalisar dattawa ta amince da 30,000 mafi karancin albashi
Majalisar dattawa ta kasa ta amince da Naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi a Najeriya.
Mahalisar ta bayyana hakan ne a zaman da ta yi a yau Talata 19 ga watan Maris .
Majalisar ta sanar da hakan ne bayan da kwamitin da aka dorawa alhakin tattaunawa kan batun karin albashi ya mika rahotonsa.