Majalisar dattawa ta mayar da wa’adin babban sufeton ‘yan sanda shekara 4

Majalisar dattawan Najeriya ta sauya dokar wanda ya cancanci ya rike mukamin shugaban sufeton ‘yan sandan kasar zuwa shekara hudu babu dadi kuma babu ragi.

Majalisar ta sauya dokar ne bayan ta yi nazari kan tsohuwar dokar ‘yan sanda ta 2004 da da kuma sauya ta zuwa ta 2020.

Da yake gabatar da rahoto kan kudurin shugaban kwamitin da ake lura da harkokin ‘yan sanda na majalisar Halliru Jika cewa ya yi, mafi yawan masu ruwa da tsaki ba su goyi bayan yadda majalisar ke tabbatar da sufetocin ‘yan sanda ya yin wani sauraren ra’ayi.

“An samu rabuwar kawuna kan wannan doka da ta bukaci tabbatar da nadin ko cire babban sufeton ‘yan sanda da majalisa ke yi,” in ji Halliru.

Dangane da naɗi ko kuma sake naɗa sefetocin ‘yan sanda a kasar majalisar za ta ci gaba da bin doron dokar da ake da shi a kasa na 215 da aka yi bayani a kundin tsarin mulki.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More