Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da kafa Cibiyar Nazarin Kan Iyakoki

Majalisar dattijai ta amince da kafa Cibiyar Nazarin kan iyaka a garin Imeko, Jihar Ogun, tare da zartar da kudiri kan hakan.
Amincewar ta biyo bayan la’akari da daukar rahoton da kwamitin kula da manyan makarantu da TETFUND suka gabatar a zaman da aka yi a ranar Laraba.
Sanata Ayo Akinyelure (PDP, Ondo ta Tsakiya), wanda ya gabatar da rahoton a madadin Shugaban Kwamitin, Ahmad Babba Kaita (APC, Katsina ta Arewa), ya ce Cibiyar za ta samar da wadanda suka kammala karatu da ilimin aiki da ka’idoji game da kula da kan iyaka don rage hadari da kalubale na barazanar da ke fuskantar kasar.
“Kafa Cibiyar za ta rage rikice-rikicen da ke kan iyakokin kasa da kuma munanan ayyukan da masu aikata laifuka ke yi”, in ji dan majalisar.
A wani lamari makamancin wannan, majalisar dattijan a ranar Laraba ma ta zartar da kudirin dokar da za ta gyara dokar Hukumar Kula da Asibitocin Orthopedic 2004
Amincewa da kudirin ya biyo bayan la’akari da rahoton da Kwamitin Lafiya (Sakandare da Manyan Makarantu) suka gabatar.
Shugaban Kwamitin, Sanata Yahaya Oloriegbe (APC, Kwara ta Tsakiya), a cikin jawabinsa, ya lura cewa “kasar tana fama da talauci da kuma tsananin nauyin cuta.”
A cewar dan majalisar, cututtukan da suka shafi jijiyoyin jiki, cututtukan kashin baya, cututtukan daji, ciwace-ciwacen daji da nakasassu na haifar da cutar ga ‘yan kasa da yawa ba tare da cikakakkiyar kulawa ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More