Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin sabon Babban Hafsan Tsaro

Majalisar dattijai a ranar Talata ta tabbatar da nadin sabon Shugaban hafsoshin tsaron (CDS) da shugabannin hafsoshin da aka tura don tantancewa da kuma tabbatarwa daga Shugaba Muhammadu Buhari.
Tabbacin ya biyo bayan gabatarwa da kuma yin la’akari da rahoton Sanata Aliyu Wamakko, na APC, na Sakkwato ta Arewa da ya jagoranci kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattijai na tsaro, sojojin sama da na ruwa.

 

Wadanda aka tabbatar su sune Manjo Janar Lucky Eluonye lrabor, Babban hafsan hafsoshin tsaro (CDS); Manjo Janar Ibrahim Attahiru, Shugaban hafsin soji (COAS); Rear Admiral Awwal Zubairu Gambo, Shugaban hafsan sojan ruwa (CNS); da Air Vice Marshal Isiaka O. Amao, Babban hafsan Sojan Sama (CAS).

 

A halin yanzu, Majalisar Dattawan ta umarci sabbin hahsoshin tsaron da su tunkari ‘yan fashi da makami da masu satar mutane.

 

A jawabinsa bayan tabbatarwa, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan wanda ya bukace su da su tunkari ‘yan fashi da makami da masu satar mutane tare da zakulo su a kan cewa lamarin ya zama kamar wani kasuwanci, inda da yawa ke cin gajiyar sa.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More