Majalisar Dattawan Najeriya ta amimnce da kasafin kudin da aka yi wa kwaskwarima

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kasafin kudin da aka yi wa kwaskwarima saboda annobar ta Covid19.

Majalisar ta amince da naira tiriliyan 10.8, sai dai ta sauya ɓangarori da dama, inda suka ƙara yawan kasafin a ma’aikatu ba kamar yadda Buhari ya gabatar musu ba a ƙarshen watan Mayu.

An samu karin naira biliyan biyar (N5,256,207,430) a kan wanda Buhari ya miƙa musu tun farko – yanzu ya zama naira tiriliyan N10,810,800,972,72 maimakon ‪N10,805,544, 664,642.

Gwamnatin Najeriya ta ce ta rage yawan kasafin ne sakamakon halin da annobar Coronavirus ta jefa tattalin arzikin nata.

Hukumomi da ma’aikatun da sauyin ya shafa:

Hukumar Tsarin Ilimin Bai-Daya: N816,517,124
Ma’aikatar Lafiya a Matakin Farko: N897,641,688
Hukumar Ci Gaban Yankin Arewa Maso Gabas: N816,517,124
Hukumar Ci Gaban Neja-Dalta: N1,743,411,240

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More