MajalIsar ta bukaci gwamnati ta saka dakar ta-baci kan hanyoyin tarayya

Majalisar dattawa ta bukaci gwamnatin tarayya ta sanya dokar ta-baci akan hanyoyin tarayya na fadin kasar ta Najeriya.

Yan majalisar dattawan sun gabatar da bukatar hakkan ne a yayin zaman majalisar dokokin na Abuja a yau Talata 15 ga watan Oktoba 2019 yayin zaman majalisar dokokin a Abuja.

 

Hakan ya biyo bayan wani jawabi da Sanata mai wakiltar Cross Riverta Kudu Gershom Bassey, ya gabatar.

 

Bassey  ya koka akan mummunan yanayin da hanyoyin tarayya ke ciki a kasar, inda ya sanarwa da majalisar dattawan cewa hukumar kula da daidaita farashin man fetur (PPPRA) ta gaza aika kaso biyar da ake chaji na famfon mai zuwa ga hukumar kula da hanoyin tarayya (FERMA) , kamar yadda aka tsara a dokar gyara hanyoyin na tarayya.

 

Da take zartar da hukunci, majalisar dattawa ta umurci kwamitin ta akan man fetur da FERMA da su binciki zargin rashin aika kudin daga PPPRA don gyara hanyoyi a kasar ta Najeriya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More