Majalisar Wakilai ta bukaci Buhari ya saki Sheikh Zakzaky

Majalisar wakilan Najeriya ta yi kira ga gwamnati da ta saki jagoran kungiyar ‘Yan Uwa Musulmi ta’yan Shi’a kamar yadda wasu kotunan kasar suka bayar da belinsa a baya.
Majalisar ta amince da wannan kuduri ne kwana guda bayan taho-mu-gamar da aka yi tsakanin ‘yan sanda da kuma mabiya Sheikh Ibrahim Elzakazaky a harabar majalisar, lamarin da ya haifar da asarar rayuka, sannan ya kai ga dage zaman majalisar.
 
 
Honourable Abdurrazak Namdas, mai magana da yawun majalisar na riko, ya shaida wa BBC cewa a matsayinsu na wakilan jama’a suna ganin ya dace a saki jagoran na ‘yan Shi’a domin wanzar da zaman lafiya.
 
 
Tun shekarar 2015 ne ake tsare da Sheikh Zakzaky bayan wani hari da jami’an tsaro suka kai wa magoya bayansa a Zariya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 300.
Tun lokacin ne kuma mabiyansa ke ta zanga-zangar neman a sako shi, suna masu zargin cewa yana cikin mummunan yanayin rashin lafiya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More