Majalisar wakilan Najeriya za ta maka Akpabio a kotu

Kakakin majalisar wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya bukaci Akawun majalisar ya gurfanar da ministan ma’aikatar Naija Delta Godswill Akpabio a gaban kotu bisa zargin yi wa ‘yan majalisa kage.

Gbajabiamila ya fitar da sanarwar hakkan ne a  shafinsa na Twitter  a yau Alhamis 23 ga watan Yuli,  bayan wa’adin sa’o’i 48 da ya bai wa Minista Akpabio na bayyana sunayen ‘yan majalisar da ya yi zargin suna karbar kwangila daga ma’aikatarsa ya wuce.

“Da safiyar yau, na umarci Akawun Majalisar Wakilai ya dauko lauyoyi, sanna ya bukace su da su shigar da karar da ta shafi aikata laifi kan Ministan (Naija Delta). A lokaci guda, za mu duba yiwuwar umartar layoyinmu su maka shi a kotu kan bata mana suna,” in ji Femi Gbajabiamila.

A farkon mako ne Mr Akpabio ya yi zargin cewa ana bai wa ‘yan majalisar dokokin tarayya kashi 60 cikin dari na kwangilolin da ake bayarwa daga hukumar raya yankin Naija Delta, wato NDDC a takaice.

Lamarin ya bata ran ‘yan majalisar inda Mista Gbajabiamila ya ba shi damar ya fallasa ‘yan majalisar da ya bai wa kwangila.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More