Malamai sun amince da hana sallar Juma’a a Kano

Malamai a jahar Kano sun amince da dakatar da sallar juma’a a daukacin masallatan jahar, a yayin da dokar hana fita ta mako daya da gwamnati ta saka don gudun yaduwar cutar, zata  fara aiki a yau Alhamis 15 ga watan Aprilu da misalin karfe 10:30 na dare.

Malaman  sun gudanar da taron  ne a Africa House da ke fadar gwamnatin Kano,karkashin kwamitin kar ta kwana na Coronavirus  da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kafa.

Shawararin malaman dai na zuwa ne bayan da hukumomi a jahar Kano suka sanar da mutuwar wani mutum mai dauke da cutar Covid 19 a jahar, yayin da adadin wadanda suka kamu da cutar suka kai mutune 21.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More