Man U ta kori PSG daga Champions League

Paris St-Germain ta yi ban kwana da gasar Champions League ta bana, bayan da Manchester United ta doke ta 3-1 a Faransa.

United ce ta fara cin kwallo ta hannun Romelu Lukaku minti biyu da fara tamaula, sai dai minti 12 tsakani Paris St-Germain ta farke ta hannun Juan Bernat.

Ana tsaka da wasa ne United ta buga kwallo ta hannun Marcus Rashford inda Buffon ya kasa rike wa, nan take Romelu Lukaku ya jefa a raga.

Daga baya ne United ta samu fenariti, kuma Marcus Rashford ya buga ya ci, kuma fenariti zai jawo cecekuce bayan da alkalin wasa ya je yaga abin da ya faru a na’urar da take taimaka masa yanke hukunci.

A wasan farko da suka fafata a Old Trafford a watan Febrairu, PSG ce ta yi nasara da ci 2-0, jumulla sun tashi 3-3 kenan, amma cin kwallo uku da United ta yi a Faransa ya ba ta damar kai wa zagayen gaba.

United ta dauki kofin Champions League sau uku a tarihi, ita kuwa Paris St Germain ba ta taba dauka ba.

Manchester United wadda take ta hudu a kan teburin Premier za ta ziyarci Arsenal ta biyar a ranar Lahadi a wasan mako na 30.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More