Martani  Rabiu Kwankwaso kan sa sauya sheka Sulaiman Bichi zuwa APC

Tsohon gwamnan  jahar Kano dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya yi magana game da juyin da aka samu a cikin tafiyar jam’iyyar PDP a jahar da kuma sauya shekar wasu dakarun Kwankwasiyya da ake ji da su aw  jam’iyyar hamayyar.

Sanata Rabiu Kwankwaso ya nuna rashin jin dadin sa   bisa sauya shekar da shugaban  jam’iyyar PDP Rabiu Sulaiman Bichi,da wasu a tafiyar ta  Kwankwasiyya  suka yi.  Inda yace ko da jariri ne ya fice daga tafiyasu, yana takaici  hakkan saboda al’umma su ne jarinsa a harkarsa ta siyasa,  kuma duk wayanda suka  hada-kai da Abdullahi Ganduje, tare da  komawa jam’iyyar ta APC ba abunda zasu samu.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a lokacin da yake hira da ‘Yan gidan rediyo a cikin daren Alhamis 23 ga watan Janairun 2020 a gidansa.

Game da zargin son kai da ake yi masa, na cewa  ya shuka irin abin da ya faru, sai ya ce ‘Ya ‘yan APC ya shuka wanda yanzu suka tofo, cewar Kwankwaso.

Ya kuma kara da cewa, duk masu cewa bai yi masu komai ba, kila duk Duniya bayan Mahaifansu, ya fi kowa tasiri a rayuwarsu.

Legit ta rawaito  cewa, a hirar an tabbatar da cewa wata daga cikin ‘Yan  tafiyar Kwankwasiyyar da ta yi mubaya’a Aisha Kaita, ta dawo daga rakiyar kwana guda da ta yi.

Mai magana da yawunsa Binta Sipikin, Kwankwaso ya ce za a iya mata uzurin sauya-sheka, saboda ma’aikaciyar gwamnati ce.

A karshe kwankwaso ya koka da abubuwan da ke faruwa a kasar tare da yin kira ga masoyan PDP su tashi tsaye a zaben kujerun majalisun da za gudanar,

duk da rashin da PDP ta yi daf da zabukan da za a sake yi a jahar, yayin da yake ganin cewa PDP ce za ta yi nasara a gobe Asabar.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More