Martanin Akpabio kan zargin lalata da Nunieh tayi masa

A kwanan -nan ne Joy Nunieh ta zargi ministan kula da harkokin Neja Delta wato Godswill da neman yin lalata da ita.

Da aka tambayi Akpabio game da zargin na Nunieh

Ga abun da yace;

Mayar da hankali a kan wasu abubuwa na daban ba shi ne ba.

“A matsayina na minista a kasar nan ba zan iya magana a kan wani mutum ba, zan iya magana ne kawai akan abinda zai kawo cigaba a yakin Neja Delta da kuma abububwa da gwamnatin tarayya zata amfana dashi , wannan
shine abinda ke daukar hankalina”. Inji ministan.

Sannan kuma ya kara da ikirarin cewa,Nunieh tana da matsalar halayya, wanda hakan ne yasa auren ta ya dingi mutuwa.

DA DUMI- DUMI : Gwamna Wike ya kubutar Nunieh daga gurin ‘yan Sanda a gidan ta

Gwamnan jahar Rivers, Nyesom Wike, ya kubutar da tsohuwar shugaban hukumar raya yankin Niger Delta wato NNDC, Joy Nunieh, a yau 16 ga watan Yuli 2020, bayan da yan sanda suka zagaye gidanta dake birnin Port Harcourt.

TVC ta rawaito cewa, gwamna Wike ya afka gidan Nunieh ta karfe, inda ya umarcin yan sandan dasu fita daga gidan, kuma ya fice da ita a cikin motarsa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More