Martanin Fasto Biodun kan zargin Fyade

Bisola Dakolo dai ta fito a wani bidiyo da ta yi hira da wani dan jarida, inda take sheda masa cewa Fasto Biodun ya yi mata fyade lokacin tana ‘yar shekara 16.

Ta kara da cewa ya yi mata fyaden ne fiye da sau daya, inda a karon farko faston ya yi lalata da ita a cikin gidansu da misalin karfe shida na safe.

Da aka tambaye ta dalilin da ya sa ba ta yi ihu ba domin jama’a su kai mata dauki sai ta ce “Ya rufe min baki.”

A yanzu Bisola mai dakin fitaccen mawakin mai suna  Timi Dakolo kuma tana da yara.

Kwatsam bayan kammala ibadar ranar Lahadi, sai Fasto Biodun ya fito ya yi wa mahalarta cocin na sa jan kunne cewa ka da su shiga rikici saboda zargin lalata mata.

Ya kara da yin kira ga magoya baya da su zama masu zaman lafiya ka da su tayar da zaune tsaye.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, faston ya ce sam bai taba yi wa wata mace fyade ba, inda ya yi barazanar kai Bisola gaban kuliya.

Ya kuma danganta ikirarin da wani yunkurin bata sunansa da na cocin.

A   kullum a kan samu yanayin da jagororin addini kan aikata wasu laifuka a matsayinsu na mutane.

To sai dai kasancewar su jagorori a addini ya sa jama’a ke mamaki da shiga dimuwa duba  cewa  mutanen wanda al’umma  suka amince da su, kuma hakan ta faru ta bangaren su.

Batun yi wa mata musamman kananan yara da matasa fyade wani abu ne da ke ci gaba da ruruwa kamar wutar daji, inda a lokuta da dama a kan samu jagororin addini cikin  irin wannan matsalar.

Kwararru kan masu tabin hankali irin su Dakta Babagana Kundi Machina, Shugaban Asibitin Kwararru na jahar Yobe da ke birnin Damaturu, sun zayyana wasu dalilai guda biyu da suka ce su ne ke sa jagororin addini yin fyade.

  • Irin yardar da ke tsakanin fasto-fasto ko malamai da mabiyansu da ke sa har su kebe musamman mata
  • Rashin fallasa matsalar fyade idan ta faru

 

Illar Fyade a cikin al’umma

  • Mutane za su iya daukar doka a hannunsu
  • Za a iya samun magoya bayan jagoran addini yin fito na fito da masu zargin sa
  • Za a iya samun mutanen da ka iya fita daga addini kasancewar

 

 

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More