Martanin PDP kan hukuncin da kotun koli ta yanke

Shugaban jam’iyyar PDP Uche Secondus, ya bayyana cewar, duk da cewa kotun koli ta yi watsi da karar da jam’iyyar da dan takararta na Shugaban kasa suka shigar akan nasarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari, hukuncin karshe na zuwa daga Allah ne.
 
Ya bukaci yan Najeriya da su cigaba da mika lamuran su ga Allah,domin kasar na cikin wani irin yanayi da sai Allah ne kadai zai iya fidda ta.
Ya yi magana ne a wani jawabi daga hadiminsa Ike Abonyi, yayinda yake martani ga hukuncin da kotun kolin ta yanke na Koran karar da suka daukaka akan nasarar shugaba Buhari da jam’iyyar APC a zaben ranar 29 ga watan Fabrairu, a yau Laraba 30 ga watan Oktoba 2910.
 
Secondus ya yaba wa yan Najeriya akan jajircewarsu da gudunmawar da suka bawa jam’iyyar da damokradiyya da kuma yaba ma yan jarida akan jajircewarsu wajen damokradiyya da shugabanci nagari a Najeriya sannan ya bukaci da kada su yi kasa a gwiwa a rawar ganin da suke takawa don mutanen kasar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More