Martanin PDP kan  hukuncin kotun koli gama da zaben Imo

Babbar Jam’iyyar adawa ta Najeriya  wato PDP, ta bayyana mamakin ta gama  da hukuncin da kotun koli ta yanke kan zaben gwamnan na jahar Imo

Talata 14 ga watana Janairu 2020 ne kotun koli ta kwace kujerar gwamna daga Emeka Ihedioha na Jam’iyyar PDP ta bawa  Hope Uzodinma na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar na 9 ga watam Maris 2019.

Bayan zartar da hukuncin kotun koli ne, kakakin jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan ya fitar  da sanarwar  cewa PDP ta gaza fahimtar dalilan da suka sa  kotun koli yanke hukuncin.

Duba da cewa  dan takarar ya zo na hudu a zaben gwamna da aka gudanar a watan Maris  da kuri’a 96,458 kuma ace ya doke dan takarar PDP da ya samu yawan kuri’u 276,404.

PDP ta ce an sauya wa mutanen Imo wanda suka zaba, an kuma basu wanda basu zaba ba.

Inda ta koka wajen cewa yanzu duk nasarorin da cigaba,  da kwanciyar hankali da aka samu karkashin gwamna Emaka Ihedioha ya fice ta rariya.

 

A karshe dai PDP tayi kira ga magoya bayanta na jahar Imo, da  su kai zuciyar su nesa tare da rungumar kaddara kan hukuncin da kotun kolin ta yanke.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More