Masalha tsakanin gwamna Ganduje da Sarki Sanusi zamu cigaba da aiki ta karkashin kasa – Ibrahim Shekarau

Tsohon gwamnan Kano, sanata Ibrahim Shekarau, ya ce yana aiki ta karkashin kasa domin ganin an samu masalaha tsakanin gwamnan Kano dakta Abdullahi Umar Ganduje da sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.

Yayin wata ziyara da ya kai ofishinmu BBC na Landan, sanatan mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, ya ce a matsayinsa na daya daga cikin ‘yan majalisar sarki kuma jigo a gwamnatin Kano ba abu ne mai yiwuwa ya fito karara yana tsokaci a kan al’amarin ba.

Dan haka za su ci gaba da aiki ta karkashin kasa domin ganin an cimma masalaha a tsakanin shugabannin biyu.

Shekarau yayi magana ne a karon farko tun bayan fara takun sakar yayin da ya cika shekarara 10 da samun sararutar Sardaunan Kano, wadda marigayi Sarki Ado Bayero ya nada shi.

“Ita masalaha kamar ciwo ce, rana daya sai ciwo ya shige ka amma sai ka shekara, shekaru ma kana shan magani ba ka warke ba,” in ji Shekarau.

Ya kuma bayyana cewa yana sane da kima da martabar masarauta, kana kuma ya san kima da martabar gwamnatin Kano don haka za su ci gaba da yunkurin ganin an sasanta.

Duk da cewa an dan samu sassauci kan bayyanar sabani tsakanin sarki da gwamna, an ci gaba da zaman ‘yan marina tsakaninsu, inda kowa yake harkarsa ba tare da shigar da dayan ba.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More