Masu garkuwa da mutane sun tuba a Adamawa

Kwamishinan yan sanda na  jahar Adamawa CP Audu Madaki, ya bayyana cewa,   kama masu garkuwa da mutane da kuma gungun yan shila da suka kayi, ya biyo baya ne bisa nasarar ta samu a lokacin da rundunan yan sandan ke mika lambar yabo ga shugabanin kungiyar Miyetti Allah, dake taimakawa a yanzu wajen zakulo masu garkuwa da jama’a da ke boye kan su cikin  daji.

Hakan yasa aka samu hadin kan da yan Miyetti Allah ke badawa a yanzu, inda ta kai ga har wayansu daga cikin masu garkuwa da mutanen guda 5 suka tuba.

Ya kara da cewa rundunan yan sandan zata cigaba da hada kai da kungiyoyin su dan a a samu cigaba wajen nasarar kau da tabargazar.

A bayanin sa kuma game da makomar wadanda suka tuban, yace za su tura wa Shelkwata kan wayanda suka tuba, da kuma wayanda aka kama, don ta bada umarnin yin hukunci a kansu .

Shugaban kungiyar Miyetti Allah na yankin Arewa maso gabas Alhaji Aliyu Abare,   ya wakilci shugaban kungiyar ta kasa, don gode musu da hadin kan da suka bayar.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More