Mata 10 sun nutse a ruwa sakamakon kifewar jirgin kwale-kwale a jahar Kebbi

Hukumar ba da agajin gaggawa ta jahar Kebbi ta ce ana zaton mata goma sun mutu sakamakon kifewar kwale-kwale a kogi a karamar hukumar Jega.

Lamarin ya rutsa da matan ne bayan sun tashi daga kauyen Gehuru zuwa wajen wani biki a wani kauye dake tsallaken kogi a jiya Litinin.

Matan sun nutse a ruwa ne sakamakon kadawar igiyar ruwa da ta kifar da kwale-kalen da suke ciki.

Shugaban hukumar ta ba da agajin gaggawa a jihar ta Kebbi Alhaji Sani Dododo ya shida wa BBC cewa an gano gawar hudu daga cikin matan, yayin da ake ci gaba na neman ragowar shidan.

Ya ce ana ci gaba da nemansu daga fadama zuwa fadama inda hanyar ruwan ke bi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More