
Mata na 4 da yara 27- Alhassan Doguwa
Dan majalisan wakilan tarayya Najeriya mai wakiltan mazabar Tudun Wada/Doguwa wato Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana cewa matansa 4 kuma sun Haifa masa yara 27 a duniya.
Doguwa ya gabatar da matan sa hudu a gaban yan majalisa yayin da ake rantsar da shi a matsayin shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan ta Najeriya, a ranar Laraba 29 ga watan Janairu 2020, ya bayyana wa takwarorin nasa cewa yana sa ran cigaba da hayayyafa wasu yaran a nan gaba. Sannan ya bayyana cewa ya kawo matansa hudu domin yan majalisa su gansu.
Ina mai farin cikin bayyana muku cewa mata na hudu na tare da ni a nan yau, inji Doguwa, sannan ya umarci matan da su mike tsaye cikin zauren na majalisa.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa wato INEC ta bayyana Alhassan Ado Doguwa a matsayin wanda ya samu nasara a zaben da aka gudanar na ranar Asabar 25 ga watan Jainaru.
Baturen zaben Farfesa Mansur Bindawa ne ya bayyana cewa, Ado Doguwa na APC ya samu kuri’u 66,667 yayin da abokin hamayyarsa Yusha’u Salisu na jam’iyyar PDP ya keda kuri’u 6,323 .
A ranar 4 ga Nuwamba 2019 ne kotun daukaka kara dake birnin Kaduna tayi kori Ado Doguwa tare da yin umarnin sake sabon zaben.