
Matar da ta sha mari gurin sanata Abbo bata bayyana a kwamitin majalisar dattawa ba
Duk da cewa biniken da majailasa take wa sanata Elisha bashi da nasaba da zargin cin zarafin, illa zargin sa da ake yi na rashin yiwa mambobinta ta da’a, duba da cewa tuni waccan maganar na hannun yan sanda.
Kwamitin wucin gadi na majalisar dattawa wanda ke bincike aka zargin cin zarafi da ake yi akan Sanata Elisha Abbo, ta bayyana cewa matar da ta sha mari gurin sanata Abbo a cikin wani bidiyo bata amsa gayyatar da aka yi mata zuwa majalisar dattawa ba.
Shugaban kwamitin Sanata Sam Egu, ya bayyana hakan ne yau Laraba a zauren majalisa inda yace duk wani kokari da aka yi don ganin wacce aka ci zarafi da mai shagon sun gurfana a gaban kwamitin ya ci tura.
Tsohon gwamnan jahar Ebonyi yace Sanatan yaki kwanta da kai a gaban kwamitin saboda yace maganar na gaban kotu. Ya kuma bayyana cewa daga kwamishinan yan sandan birnin tarayya har lauyoyin wadanda ake shari’a kansu sun ki bayar da kai bori ya hau, inda suka bayar da irin hujjar da sanatan ya bayar. Don haka, Egwu ya bukaci da a jingine lamarin zuwa wani lokacin.