Matar Sanata Kabiru Gaya ta rasu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika gaisuwar ta’aziyyar sa ga dan majalisar mai wakiltar jahar Kano ta Kudu, sanata Kabiru gaya bisa rashin maidakinsa, marigayiya hajiya Halima Gaya.

Shugaba Buhari ya bayyana marigayiya Halima a matsayin  mace mai kwazo wacce ta sadaukar da rayuwar ta a  wajen bunkasa harkokin ilimi,ya kuma yaba wa kokarin ta na kafa makarantu masu zaman kansu, wanda yana da kyau a yi kuyi da hakan. A Sanarwar da mai magana da yawun  shugaba Buhari, mallam Garba Shehu ya fitar. “Ilmi shine gishirin rayuwa a zamanin da muke, sannan  babu wata kasa da zatayi fatali dashi” inji shugaba Buhari
A karshe ya kuma jajanta wa sanata Kabiru Gaya, da al’ummar jahar Kano tare da fatan Allah ya kai rahama kabarin marigayiyar Halima Gaya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More