Matsalar fyade: Ana bincike kan mutumin da jama’ar gari suka lakada masa duka ya yi wa yar shekara 4 fyade a masallaci

Rundunar ‘yan sanda a jahar Bauchi  ta ce tana ci gaba da bincike kan wani mutum mai shekara 50, da aka kama ana zargin ya yi wa wata yarinya ‘yar shekara 4 fyade a cikin masallaci.

Wani bidiyo ya  nuna jama’ar gari sun fara kama mutumin a masallaci tare da yarinyar, inda suka lakada masa duka kafin daga bisani ‘yan sanda suka shiga cikin lamarin.

DSP Ahmad Muhammad Wakil ya fada wa BBC cewa tun ranar Alhamis ne suka kwaci mutumin daga hannun jama’a, suka kuma kai shi a kayi masa magani a asibiti.

Inda ya kara da cewa, wannan ne karo na uku da aka kama mutumin da irin wannan ta’asa.

DSP Ahmad Muhammad Wakil ya ce a shekarun 2001 da kuma 2015 mutumin ya yi zaman gidan kaso na shekaru saboda kama shi da laifin fyade, kafin gwamnati ta yi masa afuwa.

A cikin ‘yan watannin nan dai ana samun yawaitar rahotannin fyade a Najeriya.

Bidiyo daga Alhaji Dahiru Suleiman

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More