Matsalar Fyade: Dandaka ya kama a yi wa masu aikata fyaden – Ministar Abuja

Minista a ma’aikatar Birnin Tarayyar Najeriya wato Abuja, Ramatu Aliyu, ta ce tana so a rika dandake mutanen da aka samu da laifin fyade, saboda hakan ne  zai sa masu irin wannan mummunar daba’ar su ji tsoron yi wa matan fyade. “Muna so a aiwatar da wata doka da za ta tabbatar da adalci. Daure wadanda aka kama da laifin fyade bai isa ba, don haka tabbas ya kamata a rika dandake su. Idan aka kashe su, ba za su tuna komai ba, amma idan aka dandake su za su ci gaba da rayuwa amma babu kuzari,” a cewar ministar.

BBC ta rawaito cewa, ministar ta bayyana haka ne sakamakon kokawar da ‘yan kasar suke yi a baya bayan nan game da yawaitar matsalar fyade a kasar.

Masu rajin kare hakkin yara a Najeriya na ganin cewa za a ci gaba da fuskantar matsalar fyade ga kananan yara a kasar matukar gwamnati ba ta fara aiwatar da hukuncin kisa a kan masu aikata irin wannan laifi ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More