Matsalar masu garkuwa da mutane a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ta kare – Sufeto Janar na yansanda

Sufeto Janar na yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya sanar da  cewar  sun gano hanyoyin magance garkuwa da mutane da ake yi akan hanyar Kaduna zuwa Abuja

Ya tabbatar da cewar hanyar kaduna zuwa Abuja  yanzu ta gyaru kuma matafiya suna iya yin yafiyar su ba tare da wani fargaba ba.

Adamu ya bayyana wa manema labarai a lokacin da yake karin haske kan  zaman kan sha’anin tsaro da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasar a ranar Alhamis 11 ga watan Afrilu  dake babban  birnin tarayya Abuja.

A cewar Sufeto Janar , an kama da yawan masu garkuwa da mutanen, a yayin da wadansu ma sai da aka jikkata su wajen  artabunsu da jami’an tsaro a lokacin da jami’an suka kai samame a yankunan da aka fi garkuwa da mutanen.

Karshe ya kara da cewa, a yanzu yana  tabbatarwa da matafiya da ke bin hanyar Kaduna zuwa Abuja cewa yanzu hanyar lafiya lau take, sun tsarkake hanyar daga masu garkuwa da mutanen, sannan sun samu nasarar kame  masu garkuwa da mutanen  da  dama.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More