Matsalar Tsaro a Najeriya: Buhari zai yanke hukunci gama da lamarin– Buratai

Babban hafsan Sojojin kasar Najeriya, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa bai kamata a tunzura shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen daukan matakin tsige manyan hafsoshin tsaro ba, saboda shi kadai ya san inda matsalar take.

Buratai ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da ya yi da jaridar TheCable, Thisday da kuma gidan talabijin na Arise a ranar Talata, 11 ga watan Feburairu 2020,

A kwanakin baya ne majalisar dokokin Najeriya ta nemi Buhari ya salami dukkanin hafsoshin tsaron Najeriya saboda abin da suka bayyana a matsayin gazawarsu wajen kare rayukan yan kasa  Najeriya, sama ma dai Boko Haram ta karayin tasiri a kasar.

Hakkan ne yasa Laftanar Janar Buratai yace, bai kalubalance ikon majalisa ba, amma sallamar hafsoshin tsaro ba shine hanyar da zai warware matsalolin tsaro da Najeriya ke fama da it aba a  wanan lokacin.

Shugaba Buhari na sane da halin da ake ciki, kuma shi ne mai dakin, shi  kuma ya san inda ke masa yoyo, haka zalika shi kadai ne zai iya yanke hukuncin da ya kamata game da lamarin cewar Buratai.

Ban so yin magana a kan wannan lamari ba, saboda lamari ne daya shafeni kai tsaye, amma na sani duk abinda ya faru babban kwamanda shi ya san halin da ake ciki, kuma shi ne zai iya alkalanci saboda ya sainda matsalolin suke, ina ganin kamata ya yi a barshi ya yanke hukunci, ba wai a dinga ingiza shi ba.

Muna cikin wani yanayi mai sarkakiya ne, wanda ba abin wasa bane, shi yasa idan ka ce a sallami wasu shuwagabanni a Sojoji muke mamaki, saboda ba hakkan bane zai magance matsalar ba.

Ban fadi hakkan bane saboda ni ne babban hafsan Sojojin na kasa, kuma ko bana so a cire ni “A’a.

Lamarin ya wuce haka,  kuma abune daya shafi kasa, da masu kishin kasar baki daya,  masu kira a tsige hafsoshin tsaro ai daga cikinmu su ke, su ya kamata su fito da babbar murya wajen fadin abunda ake yi ba daidai ba Inji shi.

Haka zalika Buratai ya musanta batun cewa a shekarar 2009 aka fara Boko Haram, inda yace an fi shekara 30 ana watsa akidar Boko Haram a cikin al’umma, don haka abu ne mai wuya murkushe akidar gaba daya.

Sannan ya  kara nanata cewa Sojojin sun ci galaba a kan Boko Haram saboda a yanzu babu wani yankin Najeriya dake karkashin ikon su, shi yasa suka koma kai hare- haren sari ka noke don furofaganda.A karshe Buraitai  ya yi kira ga yan jaridu da suyi kokari wajen ganin basu taimaka masu ba, ta bagaren yada labaran na furofaganda

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More