Matsalar Tsaro a Najeriya: Zan nemi ganawa da shugaba Buhari – Gudaji Kazaure

 Dan majalisar wakilai Najeriya, mai wakiltar Jigawa, Muhammed Gudaji Kazaure ya bayyana cewa  matsalar tsaron ce ta hana mutane ganin ayyukan da gwamnatinsu ke aiwatarwa a  kasar ta Najeriya.

A zantawar da yayi  da BBC  Gudaji  ya bayyana cewa,zai nemi ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari don bayyana masa halin tabarbarewar tsaro da wasu yankunan kasar ke ciki.

Honorabul Gudaji Kazaure ya ce yana da hujjoji da wasu kwararan shawarwari da zai bai wa shugaba Buhari, kuma ya yi imani za su yi amfani wajen shawo kan matsalar tsaron da ake fama da shi a kasar.

A bagaren Cutar Covid19,  wacce da addabi Duniya, Gudaji Kazaure ya koka kan “yadda ake kurara cutar, (don kuwa) ba ta kai yadda ake kai ta ba”.Inji shi.

Wasu sun yi imani dan majalisar na amayar da ra’ayin ‘yan Najeriya da dama ne, inda suke zargin cewa mahukuntan kasar na bai wa annobar korona kulawar da ta fi sauran matsalolin kasar musamman ma tabarbarewar tsaro.

Dan majalisar wakilan ya ce “Ka duba ka ga yadda aka bai wa  cutar Coronavirus  muhimmanci a kowacce jaha,  karamar hukuma ta Najeriya, aka fitar da makudan kudade. Amma mutum nawa ta kashe?” Ba na shakkar tsayawa in yi magana a zauren majalisar don kawai saboda kada in yi kuskuren Turanci, Gudaji yace.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More