Matsalar Tsaro: Babban Sufeton yan’sandan Najeriya Muhammad Adamu ya isa jahar Katsina

Bayan umarnin fadar shugaban kasa,  Babban Sufeton yan’sandan Najeriya, Muhammad  Adamu  tare da mayan jami’an tsaro sun isa jahar Katsina  dan yin duba a kan yadda ayyukan samar da tsaro ke tafiya tare da samar da hadin kai tsakanin rundunar Sojoji dana yan’sanda  wajen ganin an kawo karshe  matsala tsaro da yan ta’adda a jahar,  dama sauran jahohin da yan’bindigar suka addaba.

Tawagar mayan jam’an su hada da:
darakta janar na hukumar DSS, Yusuf Magaji Bichi, mai bada shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, shugaban hukumar leken asirin kasa NIA, da sauran manyan jami’an yan’ sanda.
Mai taimakawa shugaba Buhari kan kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu  ya fitar da Sanarwa a ranar Talata  cewar,  Shugaba Muhammadu  Buhari ya bayar da umarnin samar da wata tawaga ta musamman ta ‘yan sanda da sojoji don magance rashin tsaro a jahohin Naija,  Katsina, Kaduna, Sokoto da Zamfara, ya ba da tabbacin cewa za a kara sa ido ta hanyar yin shawagi da jiragen sama da daddare, wadanda tuni aka samar da su karkashin shirin arangamar da sojoji ke yi a yankin mai taken “Operation Accord”. An kaddamar da wannan runduna ta arangamar ne mako uku da suka gabata. ”Sojojin Najeriya sun nuna za su iya a baya kuma za su sake tabbatar da cewa a wannan karon ma za su iya shawo kan matsalolin da ake fuskanta,” cewar  shugaban kasar a sanarwar.

Shugaba Buhari ya kuma bai wa al’ummar jahar Katsina hakuri da neman su bayar da goyon baya ga ayyukan soji da ke faruwa a jahar.

A karshe ya mika sakon jajensa da ta’aziyya ga wadanda suka rasa masoyansu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More