Matsalar Tsaro: Sai Yan Najeriya sun so za a kawo karshen matsalar – Buratai

Menene ra’ayinku game da hakkan?

Shugaban Rundunar Sojojin kasa ta Najeriya, Janar Yusuf Tukur Buratai ya ce ‘yan Najeriya za su iya kawo ƙarshen matsalolin tsaro da kansu tun da “su ne suke zaune da ‘yan bindigar”.

Buratai ya fadi haka ne ranar Litinin jim kaɗan bayan ya gana da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa, inda ya ce ‘yan ƙasa ba sa ba su goyon baya ta hanyar ba su bayanai amma suna zargin jami’an tsaro da gazawa.

Kafafen yada labarai a Najeriya sun ruwaito shi yana cewa satar mutane da garkuwa da su, da fashi da ta’addanci za su zo karshe ne kawai idan ‘yan Najeriya sun ga dama.
Kazalika Buratai ya ce kashi 99 cikin 100 na miyagun ‘yan Najeriya.

Magajin Garin Batsari da ke Jihar Katsina, Alhaji Tukur Mu’azu Ruma ya fada wa BBC cewa an mayar da mata kusan 600 zawarawa a garin nasa, yayin da yara kusan 2,000 suka zama marayu.

Buratai yana wannan batu ne yayin da aka kashe akalla mutum 192 cikin wata uku da suka gabata a Najeriya, a wani bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More