Matse muke da haduwa da Atiku a kotu – APC

Jam’iyyar APC ta ce a shirye ta ke ta kalubalanci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar a Kotu.

APC ta nesanta kanta da wasikar da wata kungiyar yakin neman zaben Buhari ta rubuta wacce ta nemi kasashen duniya su hana wa Atiku zuwa Kotu domin kalubalantar nasarar sake zaben shugaba Buhari

Sanarwar da Barista Festus Keyamo mai magana da yawun ofishin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ya fitar ranar Talata ta ce babu yawun jam’iyyar APC ko shugaba Buhari a matakin da kungiyar ta dauka.

Keyamo ya ce duk abin da kungiyar ta fitar bai shafi ofishin yakin neman zaben shugaban kasa ba na jam’iyyar APC ko shugaba Buhari ba.

Yakuma kara da cewa  matsu suke da  hadu da Atiku a Kotu domin tabbatar wa duniya yadda ya sha kashe a sahihin zaben da aka gudanar a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu.

Sanarwar ta ce kundin tsarin mulkin kasa ya ba Atiku damar zuwa kotu domin neman hakkinsa, kuma “Babu inda muka nemi haramta ma sa wannan ‘yancin domin ita ce kawai hanyar da mulkin dimokuradiyya ya bayar da damar gabatar da duk wani korafi”

Kungiyar yakin neman zaben Buhari da ake kira Buhari Campaign Organisation ta rubuta wasika ne zuwa ga Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka inda ta bukaci su matsawa Atiku lamba ya jingine matakinsa na kalubalantar nasarar sake zaben shugaba Buhari.

APC ta ce kungiyar tana da ‘yancin fadin albarkacin bakinta amma ba shi ne matakin jam’iyyar ba a hukumance.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More