Mawakin da yayi batanci ga Manzon Allah zai iya daukaka kara zuwa kotun koli -Ganduje

“A halin yanzu, muna jiran matakan shari’a,” in ji shi.

Ganduje ya ce an yi wa Shugaban kasar bayanin halin da ake ciki amma ya ki ya bayyana matsayin Buhari a kan lamarin.

Shariff-Aminu, mai shekara 22, wanda babbar kotun shari’ar Musulunci da ke Kano ta yanke masa hukunci kisa a watan Agustan, bayan an same shi da laifin yin sabo da aibata Manzon cikin wakar da ya saki a watan Maris.

Mawakin ta bakin lauyansa, Kola Alapinni, ya daukaka kara kan hukuncin kisan.

Alapinni ya ce dokar hukunta manyan laifuka ta jihar Kano ta 2000 ba ta da ka’ida, ba ta da amfani, kuma ya saba wa tsarin mulkin Jamhuriyar Tarayyar Najeriya (1999) kamar yadda aka yi masa kwaskwarima kuma ya keta ‘Yancin Dan Adam da kuma Bayyana Hakkokin Dan Adam na Duniya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More