MDD za ta binciki jinkirin shari’ar ‘yan Boko Haram da sauran kashe-kashe

Mai tattara bayanai ta musamman daga Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta bi kadin batun jan kafar da ake samu a shari’ar ‘yan Boko Haram, abin da har yakan kai ga mutuwar wasu daruruwa da ke tsare da su.A cikin rahoton da ta gabatar mai shafi 13, Agnes Callamard ta ce kwamitin bincike na musamman da rundunar sojin Najeriya ta kafa ya gano cewa jinkirin shari’ar da ke kai ga mutuwar daruruwan da ake zargin su ‘yan Boko Haram ne, tamkar hana musu ‘yancin samun shari’ar adalci ne.

Sai dai a cewarta kwamitin bai gano shaidar kama mutane kara-zube ba ko kuma azarbabin kashe daurarrun ba, lamarin da ya saba da zarge-zarge da dama da ta karba.

Wannan wani bangare ne na rahoton kashe-kashen azarbabi da hukuncin kisa na take-yanke da kuma kashe-kashen kara-zuba a Nijeriya da jami’ar ta gabatar mai shafi goma uku.

Jami’ar ta fitar da rahoton ne sakamakon ziyara ta mako biyu da ta kai Najeriya inda ta gudanar da bincike kan azarbabin kashe-kashen mutane da kuma hukuncin kisa na take yanke, da kuma kashe-kashen kara-zube a kasar.

Rahoton ya bi matsalolin tsaro a kasar daki-daki, kama daga rikicin Boko Haram da yadda jami’an tsaro ke tafiyar da shi, da kashe-kashen da su kansu ‘Yan Boko Haram ke yi da rikicin ‘yan fashin daji na jihohin arewa maso yamma da rikicin manoma da makiyayaa arewa ta tsakiya, da rikicin ‘yan a-waren IPOB.

Rahoton ya zargi yadda jami’an tsaro ke kamawa da azabtar da kuma azarbabin kashe ‘ya’yan kungiyar da ‘yan a-ware da kuma ‘yan Shi’a, da kuma ci-gaba da tsare jagoransu Sheik Ibrahim Zakzaky da kisan da sojoji suka yi wa mabiyansa kimanin mutum 300 a Zaria.

Haka kuma rahoton ya taba karuwar cin zarafin mata da kashe matan da ake yi, lamarin da rahoton ya ta’allaka da rashin dokar kare ‘yancin mata.

Ms Agnes ta kuma yi bayani a rahoton game da amfani da karfin kisa fiye da kima daga ‘yan sanda da sojoji, abin da ta ce ya saba da mizanin kasashen duniya da kuma rashin aiwatar da ingantaccen bincike da rashin tsari mai ma’ana na gurfanar da mutane a kotu da kuma shigar da sojoji cikin ayyukan ‘yan sanda.

Jami’ar ta ce raja’a da kasar ke yi wajen amfani da sojoji a wasu wuraren maimakon ‘yn sanda ya kawo raguwar rashin tsaro kamar a arewa maso gabas.

Amma kuma a wasu yankunan Alice Callamard ta ce lamarin ya janyo karuwar rashin yarda, ba kuma tare da an samu nasarar da ake bukata ba a yankuna da dama ciki har da tsakiyar Najeriyar.

Jami’ar ta Majalisar Dinkin Duniya, ta bayyana wa BBC cewa, tana cike da damuwa game da halin da ta samu Najeriya a ciki, inda ta bayyana lamarin kamar wata tukunyar talge mai zabalbala, wadda take ta kara tafarfasa, wadda ta ce idan ba a yi abin da ya kamata ba don shawo kan matsalar, to lamarin zai iya tarwatsewa.

Ta kuma ambato matsalar tumbatsar yawan mutane da ke rayuwa cikin talauci matsananci da yaduwar makamai da kuma gurbacewar muhalli.

Sai dai mai binciken ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce an samu raguwar kashe-kashen ba-ji-ba-gani da sojoji ke yi a yankin arewa maso gabas tun shekara ta 2016.

Sannan ta ce hukumar kare hakkin dan’adam ta Najeriya ta kara karfi duk da yake ta ce dole ne sai an martaba ‘yancinta na gashin-kai da samar wa hukumar karin abubuwa da take bukata don aiwatar da ayyukanta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More