Me kuke ganin ya kamata ayi akan Gwaggon Biri daya  Sace miliyan 7 a gidan Zoo na  Kano?

Wani abin mamaki da ya faru a cikin birnin Kano wanda yaja hankulan mutane shi ne an samu wani Gwagwaggon Biri ya lashe zunzurutun kudi har Naira Miliyan bakwai, hakan na zuwa ne biyo bayan wani labari da ya taba fita cewa Maciji, ya hadiye kudin da hukumar JAMB ta tara.

Wanda ake zargin Gorilla da lakume cinikin da aka yi a gidan Zoo na Kano a lokacin bukukuwan karamar  Sallah. Gorillan da  ake zargi an tabbatar da cewa ya hadiye Naira miliyan 7 kuma shima wannan Macijin an ce ya hadiye N35m wanda yanzu haka  Kotu ta kori macen da ake zargi akan lamarin.

A cewar BBC, babban jami’in harkokin kasuwanci gidan, Zoo din ne lokacin da yake karin bayani ya ce, “A  ranar Laraba cinikin da aka yi wanda suka kai kimanin miliyan shida, da Naira dubu dari takwas, da dubu ashirin da dubu biyu, sun bace fat wanda kudin ya samu ne daga mutanen da suka zo yawan shakatawa gidan Zoo a lokacin bikin Sallah domin kallon dabbobi.”

Gidan Radio mai suna Freedom Radio Kano, ya rawaito cewa a ranar Alhamis daya daga cikin jami’an da suke kula da wajen ajjiye kudi ya yi magana da su cewa wani babban Gorilla ya shiga Ofishin da ake ajjiye cinikin da aka yi ya gudu da shi, kuma a lokacin da ya dauki kudin ya tafi dashi wanda adadin su ya kai Naira Miliyan bakwai.

Har ila yau, a lokacin da ake tambayar sa Daraktan gidan Zoo, din Kashekobo, ya tabbatar da faruwar lamarin ga BBC, amma kuma duk da haka yace shi babu wani abu sa zai iya cewa game da wannan batu sai de kawai binciken yana ci gaba da gudana.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More