Mele Kolo Kyari ne sabon shugaban NNPC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Mele Kolo Kyari a matsayin sabon shugaban kamfanin mai na kasa Najeriya wato NNPC.

Wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin, Ndu Ughamadu, ta fitar ta ce Shugaba Buhari ya nada wasu sabbin shugabannin bangarorin kamfanin guda bakwai.

Har ya zuwa lokacin da aka nada shi sabon shugaban, Mele Kyari shi shugaban banagaren harkokin danyen mai na kamfanin, kuma tun watan Mayun 2018, shi ne wakilin Najeriya a Kungiyar kasashe masu arzikin man fetur wato OPEC.

Shugaba Buhari ya bayar da umarnin cewa sabon shugaban da sabbin shugabannin bangarorin za su yi aiki ne tare da masu rike da mukamin a baya har sai ranar 7 ga watan Yulin 2019, don tabbatar da cewa an mika aikin ba tare da wata tangarda ba.

An nada Umar Isa Ajiya a matsayin babban jami’in kula da harkokin kudi, da Adeyemi Adetunji shugaban bangaren tacewa da siyarwa.

Sannan Farouk Garba Sa’id shugaban bangaren harkokin ayyukan kamfanin.

Mista Ughamadu ya ce tsohon shugaban kamfanin Maikanti Baru ya taya sabbin shugabannin murna.

8 ga watan Yulin 2019 ake za ran sabbin shugabannin za su fara aiki.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More