Menene ra’ayiku game da soke rudunar SARS?

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce soke rundunar SARS matakine na farko cikin mataki na farko a cikin sadaukarwar na kawo sauye-sauye na ayyukan ‘yan sandan Najeriya don tabbatar da cewa jami’an tsaron sunyi aikin da ya kamata tare da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar  ‘yan kasar.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabin sa a wajen kaddamar da tsarin shirin taimaka wa matasa a fadar sa dake babban birnin Abuja.

Zanyi amfani da wannan damar wajen yin bayani  game da damuwa da tashin hankalin da aka shiga a kwanakinnan a Najeriya akan yadda wasu jami’an ‘yan sanda ke amfani da karfi tare da kashe-kashe da aiwatar da abubuwa marasa kyau ba bisa ka’ida ba.

Inda a karshe shugaban yayi alkawarin tabbatar da duk wanda aka kama da hannu cikin rashin da’a da  aikin cin zarafi zasu fuskaci shari’a.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More