Menene ra’ayin batun nada sabin ministocin a Najeriya?

96

Normal
0

false
false
false

EN-US
X-NONE
X-NONE

/* Style Definitions */
table.MsoNormalTable
{mso-style-name:”Table Normal”;
mso-tstyle-rowband-size:0;
mso-tstyle-colband-size:0;
mso-style-noshow:yes;
mso-style-priority:99;
mso-style-parent:””;
mso-padding-alt:0cm 5.4pt 0cm 5.4pt;
mso-para-margin:0cm;
mso-para-margin-bottom:.0001pt;
mso-pagination:widow-orphan;
font-size:12.0pt;
font-family:Calibri;
mso-ascii-font-family:Calibri;
mso-ascii-theme-font:minor-latin;
mso-hansi-font-family:Calibri;
mso-hansi-theme-font:minor-latin;}

Batun nadin sabbin ministoci a Najeriya na ci gaba da janyo ce-ce-ku-ce bayan rantsar da sabuwar gwamnati.

A ranar 29 ga Mayu aka sake rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a wa’adin shugabanci na biyu.

 A yanzu haka an shafe mako biyu ba tare da shugaban ya sanar da sabbin ministocinsa  da za su ja ragamar gwamnatin tasa ba.

Fadar shugaban kasar ta fito ta karyata wasu jerin sunaye da aka dinga yadawa a kafafen sadarwa na Intanet cewa su ne sabbin ministocin Buhari.

A wa’adin mulkinsa na farko, shugaban bai nada ministoci ba sai bayan kusan watanni shida da karbar ragamar mulkin kasar.

 

Yadda ‘yan kasar suka kwashe tsawon lokaci suna jira Shugaba Buhari ya bayyana ministocinsa a farkon mulkinsa, suna fatan a wannan karon ba zai yi jinkiri ba domin ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati yadda ya kamata.

Bayan zaben shugabannin sabuwar majalisa, ana tunanin shugaban ya tura sunayen ministocinsa domin fara tantance su. Sai dai ba a san lokacin da za a dauka ba  zuwa yanzu.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More