Messi ya ci kwallaye 108 a Gasar Zakarun Turai

Barcelona ta kai wasan daf da na kusa da na karshe wato quarter finals, bayan da ta doke Lyon 5-1 a karawar da suka yi a Camp Nou ranar Laraba.
Barcelona ta ci kwallayen ta hannu Lionel Messi wanda ya zura biyu a raga da wadda Coutinho da Pigue da kuma Dembele da kowannensu ya ci daidai.
Ita kuwa Lyon wadda ta tashi wasan farko a Faransa 0-0, ta shi kwallo ne ta hannun Lucas Tousart.
Kwallaye biyun da Messi ya ci ya sa yana da 108 a gasar cin kofin zakarun Turai, biye da Cristiano Ronaldo na Juventus mai 124 jumulla.
A karon farko Barcelona za ta wakilci Spaniya ita kadai tare da kungiyoyi da suka hada da Juventus da Manchester United da Manchester City da Liverpool da Tottenham da Porto da kuma Ajax.
Rabon da kungiya daya ta rage a gasar zakarun Turai irin wannan matakin tun bayan shekarar 2010, a ranar Talata ne Juventus ta fitar da Atletico Madrid a Italiya.
Rabon da ace kungiyoyin Spaniya sun kasa kai karawar daf da na kusa da na karshe tun 2005, sai dai kuma Barcelona ta hana hakan ya faru, bayan da ta kai bantenta a wasannin bana.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More