Messi zai koma yi wa Argentina tamaula

Kyaftin din tawagar kwallon kafar Argentina, Lionel Messi zai koma buga wa kasar tamaula a karon farko tun bayan gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha a 2018.

Kocin Argentina, Lionel Scaloni ne ya tabbatar cewar watakila Messi zai buga wa Argentina daya daga wasan sada zumunta da za ta yi da Venezuela ko kuma Morocco a watan nan.

Rabon da dan kwallon Barcelona ya yi wa Argentina wasa tun fitar da kasar a gasar cin kofin duniya da Faransa ta yi a wasan zagaye na biyu.

Messi shi ne ke kan gaba wajen yawan ci wa Argentina kwallaye da 65 a raga, sai dai yana shan suka cewar kokarin da yake yi a Barcelona ba ya yi wa kasarsa a lokacin tamaula.

Sai dai kuma tawagar Argentina ba ta gayyaci Sergio Aguero da Gonzalo Higuain da kuma Mauro Icardi ba.

‘Yan wasan da aka bai wa goron gayyata:

Masu tsaron raga: Agustin Marchesin da Juan Musso da Esteban Andrada da kuma Franco Armani

Masu tsaron baya: German Pezzella da Gabriel Mercado da Juan Foyth da Nicolas Otamendi da Walter Kannemann da Nicolas Tagliafico da Marcos Acuna da Gonzalo Montiel da Renzo Saravia da kuma Lisandro Martinez.

Masu buga tsakiya: Leandro Paredes da Guido Rodriguez da Giovani Lo Celso da Manuel Lanzini da Roberto Pereyra da Angel Di Maria da Matiaz Zaracho da Ivan Marcone da Domingo Blanco da kuma Rodrigo De Paul.

Masu cin kwallo: Lionel Messi da Gonzalo Martinez da Paulo Dybala da Angel Correa da Lautaro Martinez da Dario Benedetto da kuma Matias Suarez.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More