Miliyan 325 Abdulaziz Yari ya gina rijiyar birtsatsai a Zamfara

Tsohon gwamnan jahar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya musanta bar wa sabuwar gwamnatin jihar da Bello Matawalle ke jagoranta bashin makudan kudade, da kuma bayar da wasu kwangiloli na boge.

Tsohon gwamnan ya ce babu gaskiya ko kadan a cikin bayanan, kuma an yi su ne domin a bata masa suna.

Mai magana da yawunsa Malam Ibrahim Dosara ya shaida wa manema labarai a birnin Gusau cewa maganar bata da tushe bare makama.

Kwamitin karbar mulki da Gwamna Bello Matawalle ya kafa ne ya bankado wasu bayanai da suka nuna gwamnatin Yari ta bar bashin ‘yan kwangila da ya kai naira biliyan 251.

Kwamitin, wanda ke karkashin jagorancin tsohon mataimakin Yari wanda ba sa shiri yanzu, Alhaji Ibrahim Wakkala, ya kuma ce daga cikin aringizon kwangilolin da aka yi har da gina rijiyoyin burtsatse a kan naira miliyan 325 ko wacce  daya.

An dade ana ce-ce-ku-ce tsakanin kwamitin da kuma gwamnatin Yari tun bayan da jam’iyyar PDP ta dare karagar mulki sakamakon hukuncin Kotun Koli da ya soke dukkan zabukan fitar da gwani da APC ta yi a jahar, sannan ya umarni a bayyana wadanda suka yi na biyu a zabukan.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More