Ministan ayyuka ya bada umarnin sake bude Gadar Eko da Marina

Ministan ayyuka da Gidaje, Mista Babatunde Fashola, ya ba da umarnin sake bude gadar Eko da Marina don ci gaba da zirga-zirga a Legas ranar Litinin.

Fashola ya ba da wannan umarnin ne yayin da ake sa ran ma’aikatar za ta kammala kashi na farko na ayyukan gyaran gadoji a Legas da tsakar daren ranar Lahadi.

Misis Blade Akinola, mai magana da yawun ma’aikatar, ta fada a cikin wata sanarwa cewa sake budewar ya biyo bayan rahoton da kamfanin da ke kwangilar, Messrs Buildwell Plant & Equipment Industries Limited, ya bayar cewa aikin gyaran da aka yi a matakin farko an kammala shi dari bisa dari.

A cikin umarnin da ya bayar na sake bude Gadar, Fashola ya godewa ‘yan Legas bisa hakurin da suka nuna, fahimta da hadin kai yayin da aka rufe sassan Gadar.

Ya kuma bayar da umarnin cewa a sanar da jama’a game da duk wani takaita zirga-zirga yayin da aiki ke gudana a kashi na biyu na aikin.

Ministan ya kara da
cewa yayin da ya kamata a sake bude sashen da aka kammala na gadar Eko (Lagos Island Bound) don zirga-zirga, ya kamata aiki ya fara nan take a bangaren Alaka Bound.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More