Ministan Najeriya ya warke daga Coronavirus

Ministan harkokin kasar waje na kasar Najeriya, Geoffery Onyeama ya warke daga Coronavirus.

Minista Onyeama yace sakamakon gwajin da aka masa na Coronavirus ya nuna baya dauke da kwayar cutar kamar yadda  ya bayyana a shafinsa na Twitter a ranar Laraba.

Da yarda Ubangiji  sakamkon gwajin da aka mini na karshe ya nuna bani da cutar bayan daukar makonni 3 a killace, ina mutukar godiya ga iyalai na, yan uwa da abokan arziki, abokan aiki na, ma’aikatan lafiya, shugabannin  addini tare da yi masu fatan alkairi,bisa addu’o’i, azumi da kuma karfafa min gwiwa da su kayi a lokacin da nake cikin yanayin. Inji Ministan Onyeama.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More