Miyagu sun karbe  mulkar kasar Najeriya daga hannun mu- Aisha Buhari

96

Normal
0

false
false
false

EN-US
X-NONE
X-NONE

/* Style Definitions */
table.MsoNormalTable
{mso-style-name:”Table Normal”;
mso-tstyle-rowband-size:0;
mso-tstyle-colband-size:0;
mso-style-noshow:yes;
mso-style-priority:99;
mso-style-parent:””;
mso-padding-alt:0cm 5.4pt 0cm 5.4pt;
mso-para-margin:0cm;
mso-para-margin-bottom:.0001pt;
mso-pagination:widow-orphan;
font-size:12.0pt;
font-family:Calibri;
mso-ascii-font-family:Calibri;
mso-ascii-theme-font:minor-latin;
mso-hansi-font-family:Calibri;
mso-hansi-theme-font:minor-latin;}

Me zaku tufa game da furicin na Aisha Buhari? hakkan?

Matar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari,  wato Aisha Buhari ta bayyana cewa  ‘miyagun mutane’ sun karbe mulkin kasar daga hannun mutanen da ya dace su rika ‘tafiyar da ragamar mulkin kasar’ 

Aisha ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin hirar wayar tarho da aka yi da ita a wani shiri na gidan talebijin Television Continental wato (TVC).

Ta ce bai dace wadanda ya kamata su rika tafiyar da gwamnati suyi shiru ba yayin da wasu mutane ke amfani da kafafen sada zumunta suna kokarin bata sunan gwamnati.

Ta ce labaran karya da ake wallafawa sun jefa ta cikin damuwa musamman lokacin da ake rade-radin cewa shugaban kasa ya mutu da kuma lokacin da aka ce shugaban zai kara aure.

Ban dauke shi da muhimmanci ba saboda miji na ma bai san abinda ke faruwa ba game da rade-raden kara auren nasa,kawai an fara yadda labarin ne a kafafen sada zumunta. Inji Aisha.

 Ana  amfani da kafafen sada zumunta domin kawo karshen gwamnati.

 Ina tunanin bai dace mu kyale mutanen da ba su kai sun kawo ba su ci zalin ‘yan kasa na gari, Ban san dalilin da yasa mutanen da ya dace su dauki mataki suka yi shiru ba yayin da bata gari ke kwace kasar daga hannun mu, ba zai yiwu ba kuma ba zamu amince da hakan ba.

Jaridar legit ta rawaito cewa Aisha Buhari ta bayyana cewa, hadiman shugaban kasa da sauran ma’aikatan gwamnati suna watsi da muhimman abubuwan da ya dace su dauki mataki a kai, sannan suna mayar da hankali kan abubuwan da bai shafi shugaban kasa ba.

 Lokacin da ya dace  hadiman shugaban kasa su dauki mataki kan masu aikata laifuka ko su gargadi su sai su ja bakinsu suyi shiru.Amma idan abubuwan da ba su da muhimmanci ne mutane za su fara magana kan shugaban kasa.

 Misali shine abinda ya faru bayan zaben Bayelsa. Lokacin da PDP ta fito ta ce za ta dakatar da tsohon shugaba Goodluck Jonathan, kan aikata wani laifi ko wani abu mai kama da haka. “Ban ga dalilin da zai sa fadar shugaban kasa ta fito ta ce tayi mamakin jin hakan ba, domin kuwa  matsalar su can ta yan jam’iyyar PDP.

Jonathan bad an jam’iiyar mu bane, dan haka babu abunda ya hada fadar shugaban kasa da lamarin wata jam’iyya daban cewar Aisha Buhari.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More