Muhammadu Buhari zai gabatar da jawabi ga ‘yan Najeriya a yau Litinin

Sanarwar ta fito ne daga mai ba wa shugaban shawara kan harakokin yada labarai Femi Adesina.

Shugaban zai gabatar da jawabin ne da misalin karfe 7 na daren wanda za a watsa a kafofin watsa labarai na kasar.

Ana dai tunanin batun annobar coronavirus ne da kuma matakan da gwamnati ke dauka za su mamaye jawabin shugaban, inda ake sa ran watakila ya tsawaita dokar hana fita da shugaban ya kafa a jahohin Legas da Abuja da kuma Ogun.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More