Mulkin Buhari ya yi kama da na Abacha – Obasanjo

Tsohon shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya ce mulkin Buhari ya yi kama da na Abacha saboda yadda shugaban ke son ya lashe zabe ta ko wane hali.

Tsohon shugaban ya fadi haka ne a cikin wani dogon bayani mai taken “damuwa da kuma mataki” da BBC ta samu kwafi.

Obasanjo wanda ya dawo yana adawa da Buhari bayan ya goyi bayansa a zaben 2015, ya zargi hukumar zaben Najeriya INEC cewa ta shirya yin magudi a zaben 2019.

Ya ce ko INEC ta shirya yin gaskiya gwanatin APC ba za ta bari ba.

Sai dai zuwa yanzu babu martani da ya fito daga INEC da kuma bangaren gwamnatin APC wadanda Obasanjon ya zarga da shirya magudi a babban zaben da ke tafe a watan Fabrairu.

A cikin bayaninsa, Obasanjo ya kira APC da ke mulki a matsayin jam’iyyar INEC, saboda yadda take katsalandan ga harakokinta.

Obasanjo ya bada misali da zaben jahar Osun inda ya ce zaben da ba a kammala ba amma aka ce an kammala duk da hujjoji da suka tabbatar da akwai matsaloli a zaben.

“Hakan ya tabbatar da INEC na iya sanar da jam’iyyar da take so ta ci zabe ko da kuwa ta sha kaye ko kuma akwai matsaloli da za su iya sa a soke zaben ko ta ce sai an je zagaye na biyu,” in ji shi.

Ya yi kira ga ‘yan Najeriya su tashi tsaye a yaki gwamnatin Buhari kamar yadda aka yaki ta Abacha ta hanyar yin addu’o’i a masllatai da coci.

Ya ce abin da ke faruwa a zamanin Buhair ya yi kama da abin da ya faru a zamanin Abacha, inda ya ce Buhari na son ta ko wace hanya sai ya lashe zabe kamar yadda Abacha ya so ya tilaswa ‘yan Najeriya.

Janar Sani Abacha ya mulki Najeriya tsakanin watan Nuwamban 1993 zuwa watan Yunin 1998.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More