Mun yi maraba da sakamakon

Gwamnatin jihar Kano ta yaba wa kokarin hukumar INEC game da yadda ta gudanar da zabe a jihar, kamar yadda Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba ya shaida wa manema labarai.
“Da farko ya kamata a fara ne da yaba wa hukumar zabe ta INEC, saboda jajircewar da suka nuna,” in ji shi.
Daga nan ya ce za su sake yin shiri don tunkarar zabukan a mazabu a kananan hukumomi 22.
Har ila yau ya ba da tabbacin cewa ba su karaya ba.
Babban jami’in tattara sakamako zabe a Kano Farfesa B.B Shehu ne ya sanar da cewa ba a kammala zabe a Kano ba.
A cewarsa Abba Kabir Yusuf na babbar jam’iyyar hamayya PDP ya samu kuri’a 1,014,474 yayin da gwamna mai ci na Jam’iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje ya samu kuri’a 987,819.
Jam’iyyar PRP ce ta zo a matsayi na uku da kuri’a 104,009.
Ya ce kuri’u 141,694 hadi da na Gama a karamar hukumar Nasarawa wadanda aka soke daga kananan hukumomi 22.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More